05-Jun-2026
04-Jun-2026
03-Jun-2026
01-Jun-2026
20260606-Yamai
00:00
1x
Tun daga ranar 1 ga watan Mayu na bana, Sin ta soke harajin kwastam ga dukkan kasashen Afirka masu huldar diflomasiyya da ita su 53, kuma za ta habaka kayayyakin kasashen Afirka da ake shigowa da su kasar Sin ta hanyar inganta “hanya marar shinge” da sauransu. A cikin shirinmu na yau, bari mu ji ra’ayoyin masana guda hudu daga Sin da Afirka, don kara fahimtar babbar ma’ana ta matakin soke harajin kwastam da Sin ta dauka.
Tun daga ran 1 ga watan Mayun nan na shekarar 2026, kasar Sin ta kaddamar da manufar dakatar biyan harajin kwastam kan kayayyakin da ake shigowa da su kasarta daga kasashen Afirka. Wasu masanan Afirka suna ganin cewa, wannan manufa za ta taimaka wa kasashen Afirka wajen bunkasa masana'antu domin fitar da kayayyaki da aka sarrafa da kuma wadanda suke kunshe da fasahohin zamani zuwa kasuwar kasar Sin a nan gaba.
06-Jun-2026
02-Jun-2026
28-May-2026
25-May-2026
Su Qin, ita ce shugabar kungiyar agaji mai zaman kanta dake aikin ceto a kasar Sin wato Blue Sky Rescue Team, reshen Hefei babban birnin lardin Anhui na gabashin kasar Sin. Cikin shekaru sama da 10, Su Qin da sauran abokan aikinta sun kammala ayyukan ceto sama da 300, inda suka ceci rayuka da dama. Su Qin mace ce mai kamar maza yayin da take aikin ceto, tana jajircewa cikin karfin hali a lokacin da take fuskantar hadari.